Dan Majalisa Mai wakiltar Kana nan Hukumomin Arewa da Dandi a Majalisar Tarayya Garba Rabiu Kamba ya qaddamar da rabon Tallafin buhuhunan shinkafa kimanin 600 Ga Al'umma da yake wakilta.
Rabon tallafin dai ya gudana ne a daukacin kana nan hukumomin Arewa da dandi inda a karamar hukumar Arewa Sama da mutun 450 suka amfana da tallafin.
Yayinda a karamar hukumar Dandi kuwa kimanin mutun 600 ne suka amfana.
A cewar Dan Majalisan Garba Rabiu Kamba wannan na daga cikin kokarin da sukeyi na ragema al'umma radadin matsin rayuwa musamman a wannan lokaci.
Ya Kara dacewa gwamnann jaha Dr Nasir Idris Kauran gwandu tuni da ya qaddamar da rabon tallafin abincin Wanda yasa Suma suka zo da nasu domin karfafawa tareda taimakama jamaa domin ganin ansamu wadatar abinci.
Daga cikin Wadanda Suka amfana sun nuna Jin dadin su tareda godema Dan Majalisar, inda suka CE wannan bashi ne Karon farko da yake kawo goma ta arziki ba.