Kungiyar yan jarida reshen jahar kebbi ta qaddamar da rabon tallafin abinci ga iyalan ‘ya’yan kungiyar da suka rasu.
Da yake jawabi ayayin rabon abincin shugaban Kungiyar Bello sarki ya bayyana cewa wannan nada manfar ragewa iyalan radadin halin rayuwa sakamakon rashin da sukayi.
Bello sarki ya kara da cewa kimanin shekara 10 kenan da qaddamar da wannan talalfin ga iyalan mambobin kungiyar marigaya kuma kungiyar zata cigaba da wannan aiki ta tallafa musu da duk abinda ya sauwwaka.
Rabon abincin dai ya guda ne a harabar gidan talabijin mallakin jaha wanda yasamu halarcin mambobin kungiyar wakilai daga kafafen yada labarai daban daban iyalan marigayan da dai sauransu .
A nashi bangaren kwamishinan yada labarai da al’adu alhaji yakubu ahmad birnin kebbi ya jinjinawa kungiyar da wannan hangen nesa inda ya bukaci shugabannin kungiyar da su dore da wannan aikin alhairin.
Hakama kwamishinan yace zaiyi duk mai yuwa wajen ganin gwamnati ta shigo wajen bayarda tata gudumuwa ga iyalan mambobin kungiyar da suka kwanta dama domin tunawa da irin gudumuwa suka bayar wajen ciyarda jaha agaba.
Da take godiya a madadin sauran iyalan marigayan da suka amfana da tallafin uwar gidan marigayi bello ribash ta bayyana jin dadi kan wannan tallafin inda ta roki allah madaukakin sarki da ya cigaba da taimakon kungiyar da jagororinta kana da mambobin ta baki daya.
Wakilin mu ya ruwaito cewa na raba buhun shinkafa mai nauyin kilo gram 25 ga daukacin iyalan mambobin kungiyar da suka rigamu gidan gaskiya su 21 kazalika da kuma kudi naira 10,000 ga kowane inda hakama aka raba naira 80,000 da karamin buhunn shinkafa ga kungiyoyin reshen kafafen yada labarai guda 6 da sukayi rajista da kungiyar.