Matsalar Wutar Lantarki na Neman Hadamu da Abokan Hulda Fada: Masu Sana'ar Dunki.
Wutar Lantarki na da matukar muhimmanci a kowane bangare na rauywar al’umma, to sai dai karancin wutar da ake fama da shi wannan lokaci na haifar da koma baya ga masu kananan sana’o’I.
A daidai wannan lokaci da muke tunkarar bukukuwan karamar sallah, masu sana’ar dinkin tela da ke nan cikin garin birnini kebbi sun koka kan karancin wutar lantarki.
Saudat Muhammad ta jiyo mana ra’ayoyin wasu daga cikin masu sana’ar kan yanda matsalar ke shafuwar kas kasuwancin su kuma tana kan layi da cikon rahoton.
Sana’ar dunki dai nada matukar muhimmanci acikin alummah duk da irin mawuyacin halin da madunka suke shiga ciki, na rashn isashiyar wutar lantar ki, amma duk da hakan baisaka mutane sunyi kasa a guiwaba wajan ganin sunkai dunkunan su.
Wannan Kalubale na rashin isashen wutar lantarki, matsin tattalin arziki da yayi tasiri a fanin sana’ar dunki.
Yayin tattanawa da gidan rediyon Nagari Hafizu Umar Yawale wani mai sana’ar dunki Tella a Birnin Kebbi ya yi korafi dangane da wannan lamarin na rashin wada tacciyar wutar lantarki, inda yace suna cikin wadanda sukafi bukatar ta musamman ma a wannan lokacin da Al’Umman Musulmi ke kokarin sabunta tufafi domin murnar Sallah.
A cewar sa, suna fuskatan kalubale da dama wurin gudanar da ayyukan su yayinda masu kawo kayayakin su ke kukawa akan cewa, basu samun kayayakin su a lokacin da ake ce masu suzo su karba ba.
Ya kara da cewa, ko su basa jin dadi yadda suke sabama masu kawo masu dinki inda hakan ma, nasa su rasa wasu daga cikin kwastomomin su saboda Rashin cika alkawari.
Yawale, yayi anfani da wannan damar yayinda yayi kira da Hukomomin da masu ruwa da tsaki a bangaren wutar Lantarki da suyi abinda ya dace na ganin cewa an inganta sha’anin samarda wutar Lantarki, wanda hakan ko shaka babu, zai kawo sauki sosai ga masu kasuwanci akan kalubalen da suke fuskanta yayin gudanar da Kasuwancin su.
Anata bangaren Aisha Musa, mazauniya a cikin birnin kebbi, ta ce matsalar wutar lantarki, ba kadai masu sana’ar dunki ta shafa ba, suma da ke kai dunki ta shafesu,
Ta kara da cewa, bawai kadai masu dunki abin ya shafa ba hata su masu kawo dinki abin yana shafan su. Saboda ana kara masu kudin kayayakin da suka kawo sabanin in akwai wutar Lantarkin.
Inda ta ce, dole ne su kara saboda sai sun sayo Mai wanda shima yayi tsada a halin yanzu. Inda ta jadada cewa kowa na ji a jikin sa gameda Rashin isashen wutar Lantarki.
Aisha Musa tayi anfani da wannan damar inda tayi kira ga bangaren Gwamnati da Kamfanonin samarda wutar lantarkin da na raraba shi, hadi da sauran masu ruwa da tsaki a fanin wutar Lantarki da suyi abinda ya da ce na ganin cewa an shawo matsalar karacin wutar lantarki a cikin al’umma, wanda hakan zai taimaka ma kuwa da kuwa.
Masu sana’ar dunki dai da sauran al’ummar gari na kyautata zaton alamarin rashin wutar lantarki daya ke ci wa Al’umma tuwo a kwarya zai dawo daidai saboda muhimmiyar rawarda wutar lantarki take takawa ga kasuwancin su da sauran lamurran yau da kullun.