Lalle na daga cikin abubuwan kwalliya da mata ke yayi a wannan zamanin bayan kwalliyar fuska da gyaran jiki iri iri da suka zamo jiki kuma na yayi.
Ko wacce shekara ko juyi akan samu wani samfurin lalle da ake yayi tun daga kan amare har zuwa yan’mata da matan aure da kananan yara domin kara wa hannuwansu da kafafuwansu kyau, da kuma fito da kalarsu,musamman a lokacin bukukuwan sallah.
Bayan lalle na gargajiya da aka saba yi tun iyaye da kakani, akwai baki da na kwali daya shigo ya kuma samu guri zama a gun matan,musamman saboda maxa kan yaba da kyansa,wani lokacin ma har su kara da kyauta,bayan bada kudin biyan mai kunshi.
Fatima bala wata matashiya mai sana’ar lalle dake unguwar badariya tayi mana bayani akan sana’ar lalle
"Lalle yanada muhimmanci GA macce KO zamanin bikin sallah yayinda wasu kuma sunayi domin qawa, kuma KO a addininance yanada muhimmanci GA macce Wanda shine ke banbance namiji da macce kuma Yana gyara kafar Mata".
Shafa'atu Aliyu wata dattijuwa tace lalle abune mai matukar tarihi ga al’adar mallan bahaushe musamman a lokacin sallah.
"Lalle a kasar Hausa kuma a al'adance yanada matukar muhimmanci musamman ga Mata, kuma mu koda muka tashi mun ga yanda al'umma Hausawa suka dauki lalle da matukar muhimmanci, saboda an Fara lalle ne tin Daga farko anayin zube lokacin na zamani baizo ba, yanzu kuma ansamu cigaba akwai na baqi akwai na ja kuma akwai na maroon domin ado".
Shin ko akwai wata illa da lalle yake da ita ga lapiyar dan adam?
Nuruddin Haladu likita ne a Asibitin Fata na Bela a Jihar Kano, a yayin wata tattaunawarsa da Jaridar Aminiya ya ce babu wata illa da a likitance da aka taba ganowa lallen gargajiya na da shi har yanzu, sai dai dan abin da ba a rasa ba a bangaren na zamani da ake sanyawa sinadarai.
“Illar da za a iya cewa lalle na da shi sai dai ga wasu da bai karbe su ba, kamar sinadarin Haidrojin da ake sakawa a bakin lalle, sainadari ne mai karfi, ko mu a nan asibiti wanke gyambo ko wani ciwo muke yi da shi saboda kashe kwayoyin cutarsa kafin mu yi masa komai.
“To wasu idan bai karbe su ba yana sanya musu kuraje masu ruwa, ko ma kaikayi na tsawon lokaci da kashe farce yayi ta radadi, wadannan duk muna kiran su ‘allergy’.
“To banda wannan ko na zamanin gaskiya babu wata matsala ko alfanu da za mu ce lalle na da shi,”
in ji likitan.
Al’umma da dama dai sun bayyana ra’ayinsu akan muhimmanci da tasirin da lalle yake dashi a lokacin bikin saallah