Ko Barcelona zatakai zagayen daf dana karshe, tun bayan shekarar 2018/19
Tuesday, 15 Apr 2025 00:00 am

Nagari Radio

Tun shekarar da qungiyar kwallon kafa ta Sipaniya mai tashe a yanzu waton Fc Barcelona takai zagayen daf dana karshe, a gasar zakarun turai in da kara da Kungiyar kwallon kafa ta Ingila Liverpool, sai dai kash! Bayan sun doke Liverpool daci 3 - 0 da aka koma Ingila suma Liverpool suka hambbararda Barcelona daci 4 - 0.

Tun a wannan shekarar ta 2018/19 wacce Ernesto Valverde ke jagorantar Kungiyar har a wannan shekarar damuke ciki Kungiyar Kwallon kafa ta Fc Barcelona bata koma kai zagayen daf dana karsheba.

Sai dai a yaune suke da damar shafe wannan tarihi, da kuma kafa wani kyakkywan a tarihi a Kungiyar.

Yaune zasu kara da Kungiyar Kwallon kafa dake gamus watom Dortmund karo na biyu, yayinda Barcelona ke biyar Dortmund daci 4  a satin da yagabata da Dortmund takara da Barcelona a Sipaniya watom Camp Nou.

Wanda samun nasara akan Dortmund ne zai sa Barcelona tasake zuwa zagayen daf dana karshe a gasar zakarun turai.