Paris St Germain ta kai daf da karshe a Champions League, duk da rashin nasara da ta yi a hannun Aston Villa ranar Talata a Villa Park.
Aston Villa ta yi nasarar cin PSG 3-2, inda Tielemans da McGinn da kuma Konsa suka ci mata ƙwallayen a wasa na biyu zagayen kwata fainal.
Ita kuwa ta Faransa ta ci nata ƙwallayen ta hannun Hakimi da kuma Nuno Mendes.
PSG ta kai zagayen gaba da cin 5-4 gida da waje, bayan da ta yi nasarar cin 3-1 a makon jiya a Faransa.
Aston Villa ta buga Europa League a bara, wadda ta fafata a Champions League a bana, tana fatan ci gaba da zuwa gasar zakarun Turai kowacce kaka.
To sai dai Villa tana mataki na bakwai da maki 54 a teburin Premier League, bayan wasan mako na 32, kenan ba ta gurbi Champions League a baɗi kenan.
Ƙungiya biyar ce za ta wakilci Ingila a 2025/26 a Champions League kai tsaye.
Tuni PSG ta lashe kofin Ligue 1 na Faransa na bana, za ta kara wakiltar kasar a Champions League a baɗi, wadda ba ta taɓa lashe kofin zakarun Turai ba.
Ita kuwa Aston Villa ta lashe Champions League karo ɗaya a tarihi.
Aston Villa za ta kara da Newcastle United a Premier League ranar Asabar daga nan ta ziyarci Manchester City ranar Talata 22 ga watan Afirilu.