Jihar Borno - Ana zargin kungiyoyin ta'addanci watau Boko Haram da ISWAP sun ruguza gadoji biyu da bama-bamai a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kalilan bayan gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya koka kan ƙaruwar hare-haren ƴan ta'adda a jiharsa.
Rahoton jaridar Leadership ya bayyana cewa ƴan ta'adda sun fara farmakar nuhimman kayayyakin gwamnati a jihar Borno, sun fara da gadoji.
An ruwaito cewa ƴan ta'addan sun fara maida hankali kan gadoji waɗanda ke da matukar muhimmanci wajen zirga-zirgar jama'a da dakarun hukumomin tsaro a Borno. Wani dandalin tsaro da leken asiri, Eons Intelligence, ya bayyana a shafinsa na X ranar Laraba cewa hare-haren na nufin hana jami’an tsaro zirga-zirga da kuma kawo cikas ga ayyukan sojoji a yankunan da abin ya shafa. Ƴan ta'addan sun kai harin farko kan gadar Manda Fuma da ke kusa da Biu, wata hanya mai matukar amfani ga sojoji da fararen hula.
Eons Intelligence ta rubuta cewa:
"’Yan ta’adda sun fara kai hari kan muhimman gine-ginen gwamnati. Gadar Manda Fuma da ke kusa da Biu ce ta fara fuskantar wannan matsala."
Masana tsaro na ganin wannan sabon salo na kai hare-hare kan gadoji a matsayin yunkuri na kara takura wa dakarun tsaro da hana su gudanar da aiki yadda ya kamata a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.
An ruwaito cewa maharan sun tashi bam din ne da misalin karfe 2:20 na tsaƙar dare ranar 15 ga watan Afrilu, 2025. fashewar bam din ta lalata gadar gaba ɗaya, wanda hakan ya katse hanyar da ke haɗa kauyen Mandafuma da garin Biu cikin Jihar Borno.