Kamar yanda Wannam Kwamitin Faɗakarda Alhazzan jahar kebbi na KEBBI CENTRAL a wannam Shekarar ta 2025 ta fara Zagayen Ƙana nam Hukumomin Gwandu, Alieru da Jega a jiya.
Yau Alhamis ma Cikin ikon ALLAH Wannam Kwamitin na Faɗakarwa ga Maniyata Hajjin Shekarar Bana ta 2025 sun isa a ƙaramar Hukumar Mulki ta Koko/ Besse a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma'aikatar jindaɗi da wal-walar Alhazzai na jahar kebbi wato Alh.Faruku Aliyu Enabo (Jagaban Gwandu), kamar yanda Maigirma Gwamnan jahar kebbi HE.Comrd.Dr.Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya Umartar ayi domin tabbatarda Alhazzan jahar kebbi sun samu gudanarda Aikin Hajji cikin Nasara.
Yau ma wannam Kwamitin yana tare da Jagororinsa waɗanda suka haɗa da Alh.Amadu Bala, Alh.Umar Ɗan Bk, Mal.Aminu Hassan, da dai sauran Ma'aikatan wannam Kwamiti Maza da Mata domin isarda saƙon da Shugaban Hukumar Alhazzai ta jahar kebbi ya bayar.
Wannam Kwamitin yana tare da Malamai na Musamman domin faɗakarda Waɗannam Maniyata Aikin Hajji, domin yin wa'azi tare da kira ga Maniyatan domin suzamo masu Ɗa'a da Biyayya kamar yanda aka san Al'ummar jahar kebbi da Tarbiya a duk inda sukaje .
Wannam Kwamitin yiwa Maniyatan Albishir da cewa Maigirma Gwamnan jahar kebbi HE.Comrd.Dr.Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) yace ashaidawa Alhazzan da cewa ya Ɗauke musu biyan Kuɗin HADAYA da Kuɗin HARAMI.
Haka zalika suma Matan Maigirma Gwamna Her Excellency Haj.Zainab Nasare Nasir (Ƙauran Gwandu), da Her.Haj.Nafisa Nasir (Ƙauran Gwandu) sun ɗauki nauyin sayema Maniyata Mata Tufafinda zasusa (Uniform).
Daga ƙarshe anyi addu'ar ALLAH yayiwa Maigirma Gwamnan jahar kebbi HE.Comrd.Dr.Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) tare da Shugaban Hukumar Alhazzai ta jahar kebbi Alh.Faruku Aliyu Yaro Enabo (Jagaban Gwandu) akam ALLAH yasaka musu da Alkhairi bisa ƙoƙarinda sukeyi wajen samarwa da Alhazzan jahar kebbi Sauƙi da Wal-wala alokacin Aikin Hajji.
Daga:-
Hajj Media Team 2025
KEBBI CENTRAL
Pilgrims Walfare Agency