Manchester United ta kai zagayen kusa da ƙarshe a gasar zakarun Turai ta Europa League bayan doke Olympic Lyon ta Faransa 5-4.
Man United ce ta fara cin ƙwallo biyu tun kafin hutun rabin lokaci, kafin Lyon ta farke su, wanda ya sa aka tafi ƙarin lokaci.
A nan ne kuma Cherki ya ci wa Lyon ta uku, sannan Lacazette ya ci ta huɗu. Daga nan ne kuma Mainoo ya yi kukan kura ya farke ɗaya, shi ma Magiure ya jefa ta biyar a mintunan ƙarshe.
Kenan wasa ya tashi 7-6 gida da waje, bayan buga 2-2 a Faransa.
Ita ma Tottenham ta yi nasarar kaiwa zagayen semi fayinal bayan doke Eintracht Frankfurt 1-0, wasa ya tashi 2-1 kenan gida da waje.
Finaretin da Dominic Solanke ya ci tun kafin hutun rabin lokaci, ita ce ta bai wa Spurs nasarar.