Me ya sa batun goyon bayan Tinubu ke raba kan makusantan Buhari?
Saturday, 19 Apr 2025 00:00 am

Nagari Radio

A wani lamari mai kama da na ba-zata a fagen siyasar Najeriya, sunan tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya sake dawowa yake amo, musamman bayan alamu sun fara nuna akwai ɓaraka a tsakanin makusantansa.

 

Alamu sun fara bayyana ne a lokacin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar SDP, inda ya ce da amincewar tsohon shugaban ƙasar ya sauya sheƙar ta siyasa.

 

Sai dai daga baya Buhari ya fito ta bakin kakakinsa, Garba Shehu, cewa shi ɗan APC ne, kuma yana alfahari da kasancewarsa ɗan jam'iyyar, inda ya ce yana godiya ga magoya bayan APC, sannan zai yi duk mai yiwuwa domin samun nasararta.

 

Sai dai daga lokacin aka samu wata goguwar siyasa ta tashi a ƙasar, inda aka fara maganar jiga-jigan ƴansiyasar ƙasar za su koma SDP domin a samu haɗakar da za ta ƙalubalanci APC.

 

Abin da ya jawo ɓarakar - Masani

A game da yadda lamarin yake tafiya, BBC ta tuntuɓi mai sharhi kan harkokin yau da kullum da siyasa a Najeriya, Bashir Hassan Jantile, kan yadda aka fara ganin ɓaraka a tsakanin makusantan na Buhari, wanda ya ce al'amari ne mai sauƙin fahimta.

 

A cewarsa, "a ganina babu wata dambarwa, domin kowa yana bayani ne a matsayin da yake kai. Misali Faruk Adamu Aliyu ai babu jayayya idan aka yi maganar Buhari a shekara 20 da suka gabata su ne a gaba a cikin abokan tafiyarsa."

 

Sai dai ya ce yanzu abubuwa sun canja, inda a cewar Jantile daga lokacin da Buhari ya hau mulki, ya yi shekara takwas zuwa yanzu akwai wasu jiga-jigan da suka fi kusanci da shi.

 

"Idan ana maganar Buhari a yanzu, matuƙar ba ka ga Isa Ali Pantami ba ko Hadi Sirika ba ko Abubakar Malami ba, to wannan wasa ne kawai," in ji shi.

 

A game da zargin cewa tsagin da suka nuna goyon bayansu ga gwamnatin Tinubun suna da wata alaƙa da gwamnatin ne, Jantile ya ce hakan ne ma ya sa bai ga laifinsu ba don sun kare gwamnatin.

 

"Abin da suka yi, sun yi daidai, amma ba su da ƙarfin su Malami a wajen Buhari a yanzu."

 

A game da inda matsalar ta fito, Jantile ya ce Bola Tinubu ne tushen dambarwar tun a farko.

 

"Shugaba Bola Tinubu ba ya ya yin wasu abubuwa na zahiri tare da Buhari. Misali a zamanin Buhari akwai sanannun yaran Tinubu irin su Osinbajo da Fashola a gwamnati, amma a yanzu babu yaran Buhari a gwamnatin Tinubu."