Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaron ƙasar su gaggauta kawo ƙarshen matsalar tsaro da take ƙara ƙamari a jihohin Borno da Plateau da Benue da kuma Kwara.
Wannan na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya gana da shugabannin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja, inda suka yi nazari a kan yanayin tsaro a Najeriya.
A wata sanarwa da ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriyan, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya bayyana damuwa kan kisan ƴan Najeriya da basu ji ba, ba su gani ba a sassan ƙasar.
Shugaban ƙasan wanda ya shafe fiye da sa'oi biyu yana ganawa da shugabannin hukumomin tsaron Najeriya, ya ce dole ne su kawo ƙarshen kisan mutane a ƙasar.
Sanawar ta ayyano shugaba Tinubu yana shaidawa hafsashin tsaron cewa daga ɓangarensa fa tura ta riga ta kai bango, domin haka wajibi ne su tashi tsaye domin samar da mafita game da halin da Najeriya ke ciki a kan tsaro.
Dama dai shugaban ƙasar ya umarci shugabannin tsaron su yi aiki tare da hukumomin jihohin da ke da matsalolin tsaro a Najeriya domin cimma matsaya a kan matakin bai ɗaya da ya fi dacewa a ɗauka a kai tun daga tsuhe.
A kan haka ne kuma shugabannin hukumomin tsaron suka sake komawa domin yi wa shugaba Tinubu bayanin abubuwan da suka gano kawo yanzu.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara a kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce a yayin taron na jiya Laraba, an yi kyakkyawan Nazari game da matsalolin tsaron ƙasar da ma matakan da ya kamata a ɗauka a kai.
Ya ce: "A wannan karon mun zauna da shugaban kasa kuma mun shafe sa'oi muna yi masa bayani dalla-dalla. Yayin da kuma muka amsa sabbin umarnin a kan ayyukan tabbatar da tsaro.
"Shugaban ƙasar na aiki tuƙuru domin ganin ƴan Najeriya suna rayuwa cikin kwanciyar hankali da tsaro. Ba za mu gajiya ba har sai mun cimma burin mu na samar da tsaro ga jama'a.''
A game da dawowar hare-haren Boko Haram a jihar Borno kuwa, Malam Nuhu Ribadu ya ce "Maƙiyan namu ba su miƙa wuya cikin sauƙi. Kuma suna mafani da dabarun kai hare-hare ne domin nuna cewa har yanzu suna nan da ƙarfin su, da kuma sanya tsaro a zukatan mutane.''
A baya bayan nan ana fama da matsalolin rashin tsaro da a Najeriya; daga hare-haren Boko Haram da na ƴan bindiga a arewa maso yamma da rikicin jihar Plateau da kuma ayyukan ƴan bindiga a jihohin
Kwara da kuma Niger.