Barcelona ta samu nasarar ɗaukar Copa del Rey na 31 jimilla bayan cin Real Madrid
Sunday, 27 Apr 2025 00:00 am

Nagari Radio

Barcelona ta lashe Copa del Rey na 31 jimilla, bayan doke Real Madrid 3-2 ranar Asabar a Estadio Olímpico da ke birnin Sevilla a Sifaniya.

 

Barcelona ta fara cin ƙwallo ta hannun Pedri a minti na 28 da take leda, kuma na biyu a Copa del Rey, sannan na farko tun bayan wadda ya zura a ragar Atletico Madrid cikin Fabrairu.

 

Daga baya Real Madrid ta farke ta hannun Kylian Mbappe a bugun tazara, saura minti 20 a tashi daga wasan na El Clasico.

 

Real ta kara na biyu ta hannun Aurelien Tchouameni, amma Barcelona ta farke ta hannun Ferran Torres, saura minti shida a tashi karawar.

 

Alkalin wasa ya bai wa Barcelona fenariti, bayan da Raul Asensio ya yi wa Raphinha keta a da'ira ta 18, daga baya aka soke bayan tuntuɓar VAR.

 

Haka suka tashi min 90 da ɗan karin lokaci suna 2-2, daga nan aka je karin lokacin minti 30, inda minti 15 ɗin farko sakamakon bai canja ba.

 

A mintin 15 na biyu ne a cikin karin lokaci, Barcelona ta kara na uku a raga ta hannun Jules Kounde, saura minti biyar a tashi fafatawar.

 

An bai wa Antonio Rudiger da kuma Lucas Vázquez jan kati a karawar ta manyan ƙungiyoyin Sifaniya.

 

Wasan karshe na takwas kenan da suka kara a Copa del Rey a tarihi, inda kowacce ta yi nasara lashe shi sau huɗu.

 

Wannan shi ne karo na uku da suka haɗu a gasa a kakar nan, inda Barcelona ta je ta doke Real Madrid 4-0 a La Liga a Santiago Bernabeu cikin Oktoban 2024.

 

Haka kuma dai Barcelona ta lashe Spanish Super Cup a kan Real Madrid da cin 5-2 a Saudiyya a cikin watan Janairun 2025.

 

Za su kara fafatawa nan gab a watan gobe, inda Barcelona za ta karɓi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu a La Liga ranar 11 ga watan Mayu.

 

Wannan shi ne Copa del Rey na 31 da Barcelona ta ɗauka, ita ce kan gaba a yawan lashe shi, sai Athletic Bilbao mai 24 da kuma Real mai 20 jimilla.

 

Tuni dai aka yi waje da Real Madrid a Champions League a hannun Arsenal, ita kuwa Barcelona za ta buga daf da karshe da Inter Milan.

 

Barcelona ce kan gaba a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid mai rike da kofin bara.