Yayin da duniya ke murnar Ranar Ma'aikata a kowace ranar 1 ga watan Mayu, ma'aikatan Najeriya na cikin wani hali na damuwa da tashin hankali.
An ware wannan ranar ne domin girmama ƙoƙarin ma'aikata a duniya, amma ga ma'aikatan Najeriya, wannan rana na tuna musu da matsalolin da suke fuskanta a kowace rana.
Waɗannan matsaloli sun haɗa da ƙarancin albashi da wahalar rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi da wahala wajen aiki da kuma rashin ingantattun yanayin aiki da dai sauran su.
Yawanci ma'aikata a Najeriya suna bayyana takaicinsu dangane da yanayin da suke ciki a ƙasar.