Kamfanin Dangote ya sanar da buɗe damar shiga shirin horar da matasa ‘yan Najeriya da suka kammala karatun jami’a ko HND. Shirin dama ce ga sababbin masu digiri ko babbar difloma ta HND da ke neman samun ƙwarewa da gogewa a fannin aiki.
Shirin na 2025 ya ƙunshi horo na musamman da zai taimaka wajen haɓaka ƙwarewa da gina kwarewar aiki cikin yanayi na hadin gwiwa da koyo daga kwararru. Sharudan daukar matasa a kamfanin Dangote Daga cikin sharuddan shiga shirin akwai kasancewa dan shekaru 28 ko ƙasa da hakan a lokacin neman gurbin aikin. Haka kuma, dole ne mutum ya mallaki kwalin digiri da mafi ƙarancin darajarsa ta kai Second Class Lower daga jami’a ko Upper Credit daga HND. Kamfanin ya kuma bayyana cewa dole ne mai neman gurbin ya gabatar da takardar shaidar kammala NYSC ko takardar sallama daga wadanda ba su yi hidimar ba.
Dangote na gina rayuwar miliyoyi mutane A cewar kamfanin, babban burinsu shi ne tallafa wa mutane ta hanyar samar da kayayyakin bukatun a yau da kullum da kuma raya kasashe musamman a yankin Afrika.