A kakar ƙwallon ƙafa 2024-25, wadda ke gab da ƙarewa, an ga ƴan ƙwallo gwaraza da suka nuna bajintarsu a ƙungiyoyi manya da dama, da ma waɗanda suke ƙwallo a ƙananan ƙungiyoyi.
Sai dai wani abu da ake magana shi ne ganin yadda aka samu matasan ƴanƙwallo da suka samu damarmaki har suka fara nuna ƙwarewa a cikin manyan ƴanwasa a manyan ƙungiyoyi.
A baya, akwai manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na duniya da ake ganin sai gwanaye kawai ke iya zuwa, ko da kuwa sun je, sai dai zaman benci suna jiran lokacin da manyan za su matsa su ba su wuri.
Sannan an sha ganin matashin ɗan ƙwallo da yake fitowa da ƙarfinsa, ya fara tashe, amma kwatsam sai a neme shi a rasa, ko dai raunuka sun hana shi sakat, ko kuma tauraronsa ya dusashe cikin ƙanƙanin lokaci.
Lamine Yamal
Asalin sunansa Lamine Yamal Nasraoui Ebana wanda aka haifa a ranar 13 ga watan Yulin shekarar 2007. Ke nan dududu har yanzu shekarunsa 17, amma sunansa ya karaɗe duniyar ƙwallon ƙafa.
Ɗanwasan na ƙungiyar Barcelona da tawagar ƙasar Spain tuni aka fara masa kallon magajin Messi, saboda yadda yake nuna ƙwarewa da bajinta wajen taka leda da zura ƙwallaye.
Ya zuwa yanzu daga shekarar 2023 da ya fara buga wa Barcelona ƙwallo, ya buga wasa 72, ya zura ƙwallo 14, sannan ya buga wa tawagar Spain wasa 19, ya zura ƙwallo 4.
Ya lashe kofin La Liga biyu, sannan ya lashe kofin Copa del Rey da kofin Supercopa de España a Barcelona.
Sannan ya lashe kofin gasar nahiyar turai a Spain, inda ya lashe kambun gwarzon matashin ɗan ƙwallon gasar.
Ganin yadda ya samu waɗannan nasarorin a ƙasa da shekara 18, wanda ake tunanin lokacin ne ake fara tashe, ya sa ake hasashen cewa nan gaba za a sha kallo daga matashin ɗanwasan.
Arda Güler
Arda Güler ɗanwasan tawagar ƙasar Turkey ne da ƙungiyar Real Madrid ta Spain wanda aka haifa a ranar 25 da watan Fabrairun shekarar 2005.
Zuwa yanzu matashin ɗanwasan shekarunsa 20 a duniya, amma tun baya tauraronsa ya fara tashe, har wasu ke ganin ya kamata a ƙara masa lokacin da yake samu a wasannin ƙungiyar Real Madrid.
Matashin yana nuna ƙwarewa wajen iya rarraba ƙwallo da taimakawa a zura ta a raga.
Daga kakar 2023 da ya koma Madrid zuwa yanzu, ya buga wasa 37 ya zura ƙwallo 9, sannan a tawagar Turkiyya ya buga wasa 32 ya zura ƙwallo 7.
Ya lashe kofin gasar kofin Turkiyya a Fenerbahçe a kakar 2022–23.
A Real Madrid kuma ya lashe gasar zakarun turai da La Liga da sauran su.
Amad Diallo
Amad Diallo shi ma matashin ɗanƙwallo ne da ake ganin yana tashe sosai a yanzu duk da ƙarancin shekarunsa.
An haife shi a ranar 11 ga watan Yulin shekarar 2002 a ƙasar Ivory Coast, kuma yanzu yake wakiltar tawagar ƙasar da ƙungiyar Manchester United ta Ingila, inda ake masa kallon ɗaya daga cikin zaratan ƴanƙwallon ƙungiyar musamman a tsakanin shekaru biyu da suka gabata zuwa yanzu.
A shekarar 2021 ce Man United ta ɗauko Diallo daga ƙungiyar Atalanta ta Italiya, amma ta tura shi aro zuwa ƙungiyar Rangers a shekarar 2022, sannan ta sake tura shi aro a ƙungiyar Sunderland ta Ingila a shekarar 2023, inda ya buga wasa 37, ya zura ƙwallo 13, kafin ya dawo ƙungiyarsa ta asali.
Ya lashe kofin FA a Manchester United a kakar 2023–24, sannan ya lashe kofin gasar Scotland a Rangers.
Shi ma ɗanwasan mai shekara 22 ana ganin tauraronsa zai cigaba da haskawa zuwa gaba.
Pau Cubarsí Paredes
Pau Cubarsí Paredes ɗan wasan ƙungiyar Barcelona ne da aka haifa a ranar 22 ga watan Janairun 2007.
Ɗanwasan na tawagar Spain yana cikin matasan ƴanƙwallo da ake ganin taurarinsu na ƙyalƙyali, musamman ganin shekarunsa 18, amma kuma ya kasance cikin ƴanwasan da ke samun lokaci sosai a Barcelona.
Zuwa yanzu ɗanwasan na baya ya buga wa Barcelona wasa 51 a wannan kakar da aka mayar da shi babbar ƙungiyar, sannan ya buga wa babbar tawagar Spain wasa 6 a wannan shekarar.
Wannan ya sa shi me ake kallon zai cigaba da jan zarensa zuwa wani lokaci.
Myles Anthony Lewis-Skelly
Myles Anthony Lewis-Skelly ɗanwasan tsakiya ne da ke wakiltar tawagar ƙasar Ingila da ƙungiyar Arsenal ta Ingila.
An haife shi ne a ranar 26 ga watan Satumban shekarar 2006, sannan ya fara buga ƙwallo a babbar ƙungiyar ta Arsenal ne a kakar bana ta 2024-2025, sannan ya samu damar shiga cikin ƴanwasan babbar tawagar ƙasar.
Ya yi fice wajen kwantar da hankali a lokacin da ake wasa, inda ba ya fargabar riƙe ƙwallo ya ratsa tsakiyan manyan ƴan wasa gaba-gaɗi.
Zuwa yanzu ya buga wa Arsenal wasa 22, ya zura ƙwallo 1, sannan ya buga wa Ingila wasa biyu, ya zura ƙwallo ɗaya.
Shi ma dai ana ganin tauraronsa zai haskaka saboda yadda ake kallon shekararsa 18 a yanzu
Dean Huijsen
Asalin sunansa Dean Donny Huijsen Wijsmuller wanda aka haifa ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2005.
Ɗanwasan baya ne da yake wakiltar ƙasar Spain da ƙungiyar AFC Bournemouth ta Ingila.
Sai dai ƙungiyar Real Madrid ta sayi ɗanwasan a ranar 1 ga watan Yulin wannan shekarar ta 2025, bayan bajintar da ya nuna.
Ya buga wa ƙungiyar Bournemouth wasa 30, ya zura ƙwallo uku, sannan ya buga wa babbar tawagar Spain wasa 2.
Ganin yadda Madird ta ɗauko matashin ɗanwasan mai shekara 20 ya sa ake ganin hankali zai ƙara komawa kansa.
Désiré Nonka-Maho Doué
shi ma wani matashin ne da tauraronsa ke haskawa a yanzu a harkar tamaula.
An haife shi ne a ranar 3 ga watan Yunin 2005, kuma yana wakiltar tawagar ƙasar Faransa ne da kuma ƙungiyar PSG.
Matashin mai shekara 19 ya buga wa PSG wasa 31, inda ya zura ƙwallo shida, sannan ya fara wakiltar babbar tawagar Faransa.