Ƙasar Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makaman da kuɗinsu ya kai Dala miliyan 346, kwatankwacin Naira biliyan 530 don yaƙi da ta’addanci.
Makaman da za a siyar sun haɗa da bama-bamai da na’urorin kakkabo jiragen sama da jirage marasa matuka da sauran su.
A cewar Kamfanin Sarrafa Makamai na Amurka (DSCA), za a sayar wa Najeriya makaman ne domin tallafa wa shirinta na yaki da ’yan ta’adda da masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Kamfanin ya sanar da cinikin ne a cikin wata sanarwa ranar Laraba.
A cewar sanarwar, Najeriya ta buƙaci sayen bama-bamai guda 1,002, na’urar kakkabo jirage guda 1,002, sai manyan bindigu guda guda 5,000 da sauran makamai.
Kazalika, Amurkar ta amince ta sayar wa Najeriya helikwaftocin kai hari guda 12 da sauran muggan makaman da darajarsu ta kai Dala miliyan 997 a 2022.
Kamfanin ya ce kamfanonin da aka amince wa su yi kwangilar dillancin makaman su ne Lockheed Martin da RTX.N da kuma BAE.
“Wannan cinikin zai taimaka wa bunƙasa hulɗar kasa da kasa da kuma manufofin Amurka a kan harkar tsaro da inganta alaƙa da Najeriya a matsayin babbar ƙawa a yanki Afirka yamma da hamadar Sahara,” in ji sanarwar.