Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ɗan Bindiga, Abubakar Abba.
Thursday, 14 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Kyaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta ce har yanzu ba a ba su dala 100,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi musu alƙawari bayan sun lashe gasar WAFCON a ƙasar Maroko ba.

Ajibade, ta bayyana takaicinta game da jinkirin biyan kuɗin da aka musu alƙawari.

“Ba mu karɓi kuɗin ba tukunna, amma ina fata za a biya mu. Duk alƙawuran da aka mana, yanzu dai ba mu samu komai ba.”

Ajibade ta jagoranci tawagar zuwa ga nasara, inda suka sake lashe kofin WAFCON a bana.

Bayan nasarar, Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan da masu horar da su lambar yabo ta ƙasa (Officer of the Order of Niger – OON).

Haka kuma ya yi musu alƙawarin bai wa kowannensu dalar Amurka 100,000 da gida mai ɗaki uku.

Lokacin da ya karɓe su a Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya yaba da jajircewarsu, da kuma ƙoƙarinsu, inda ya ce nasararsu ta ɗaga mutuncin Najeriya.