Janar Tiani ya kori shugaban kungiyar alkalai ta Nijar(SAMAN)
Thursday, 14 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

 

Janar Tiani ya kori shugaban kungiyar alkalai ta Nijar(SAMAN)

 

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar ABDOURAHAMANE Tiani ya kori Abdoul-Nasser Bagna Abdourahaman daya daga cikin alkalan Nijar kuma babban sakataren kungiyar alkalai ta Nijar SAMAN bayan matakin rusa kungiyar da sojojin kasar suka yi a makon da ya gabata.

A ranar 7 ga wannan wata na Agusta ne ministan cikin gida ya dauki matakin rusa wadansu kungiyoyi uku na kwadago na sashen ma'aikatar shari'a ciki har da kungiyar ta SAMAN.

Sai dai kungiyar ta garzaya kotu domin kalubalantar matakin hukumomin kasar wanda ta ce ya saba da 'yancin aikin kungiyoyin kwadago