Peter Obi ya buƙaci magoya bayansa su zaɓa ADC a zaɓukan cike gurbin Najeriya
Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a Jam'iyyar Labour, Peter Obi ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri'a a Najeriya, musamman masoyansa na ƙungiyar Obidient da su zaɓi jam'iyyar ADC ne a zaɓukan cike gurbi da za a yi a gobe Asabar.