Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa ƙimar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22?aka samu a watan Yuni 2025. Wannan na nuni da raguwa da kashi 0.34% idan aka kwatanta da watan da y
Friday, 15 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa ƙimar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22?aka samu a watan Yuni 2025. Wannan na nuni da raguwa da kashi 0.34% idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin abinci na shekara-shekara a watan Yuli 2025 ya kai kashi 22.74%, wanda ya ragu da maki 16.79% idan aka kwatanta da kashi 39.53?aka samu a Yulin 2024. NBS ta danganta wannan raguwa mai yawa da sauyin shekarar wajen lissafi.

A kan lissafin wata-wata, hauhawar farashin abinci a watan Yuli 2025 ya tsaya a kashi 3.12%, raguwa da kashi 0.14?ga kashi 3.25% na watan Yuni 2025. Hukumar ta ce hakan ya samo asali ne daga saukar farashin man gyaɗa, da wake fari, da shinkafar gida, da masara, da fulawa, da dawa, da alkama da sauran su.

Sai dai a fannin hauhawar farashin gaba ɗaya, rahoton ya nuna cewa a watan Yuli 2025 an samu ƙarin kashi 1.99% idan aka kwatanta da kashi 1.68% na watan Yuni 2025, ma’ana ƙimar hauhawar farashin wata-wata da ta fi ta watan da ya gabata.