Jami'an tsaron farin kaya a jihar Kaduna sun kama Shehu Aliyu Patangi da tsabar kuɗi kimanin miliyan 30 da niyyar zuwa sayen ƙuri'a
Saturday, 16 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

DA DUMI-DUMI: Jami'an tsaron farin kaya a jihar Kaduna sun kama Shehu Aliyu Patangi da tsabar kuɗi kimanin miliyan 30 da niyyar zuwa sayen ƙuri'a yayin zaɓen cike gibi da za'a gudanar yau na ɗan majalisar wakilai mai wakiltar chikun/Kajuru a jihar.

Misalin ƙarfe 3 na daren jiya jami'an suka damƙe shi a wani sanannen Otel dake cikin garin Kaduna.