
Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa mutane 62 da aka yi garkuwa da su sun samu nasarar tserewa, bayan luguden wuta da jirgin yaki na soji yayi a sansanin fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Muhammadu Fulani, da ke karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.
Kakakin ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar, Dakta Nasir Mu’azu, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Katsina.