Gwamnatin Najeriya ta dauke wa maniyyatan Kiristoci masu san zuwa ibada jerusalem rabin kuɗin kujera~ DW
Monday, 18 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Hukumar Shirya Ziyarar Ibadar Kiristoci ta Najeriya (NCPC) ta tabbatar da cewa za a ci gaba da aikin hajjin Kirista zuwa Isra’ila da Jordan a watan Satumba, bayan dakatar da shi da aka yi sakamakon rikicin da ya kunno kai a Gabas ta Tsakiya. Babban Sakataren Hukumar, Bishop Stephen Adegbite, ya bayyana hakan bayan dawowarsa daga Isra’ila, inda ya tabbatar da cewa yankin yanzu ya samu nutsuwa.

Jaridar Punch wacce ta ruwaito labarin ta ce Adegbite ya ce Gwamnatin Tarayya ta amince da rage kuɗin kujerar zuwa ibadar ta Kirista da kashi 50%, wanda hakan ke nufin cewa masu niyya za su biya rabin kuɗin kawai. Ya ƙara da cewa aikin zai ɗauki kwanaki goma, kuma za a kaddamar da shi ne a ranar 14 ga Satumba, 2025 daga jihar Imo.