GWAMNA IDRIS YA KIRKIRO KWAMITI DON BIBIYA DA TANTANCE BARNAR DA RUWAN AMBALIYA YA YI A JIHAR KEBBI
Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu), ya amince da kafa wani kwamiti mai karfi domin duba da tantance irin barnar da ambaliya ta haifar a fannoni daban-daban na ayyukan more rayuwa a fadin jihar.
An nada Kwamishinan Ayyuka, Injiniya Abdullahi Umar Faruq (Muslim), a matsayin shugaban kwamitin. Ayyukan kwamitin sun hada da ziyartar wuraren da abin ya shafa, tattara shaidun barnar, da kuma bayar da shawarwari kan gyara da sake gina muhimman ababen more rayuwa da ambaliya ta lalata.
Mambobin kwamitin sun hada da:
Kwamishinan Yada Labarai, *Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi
Kwamishinan Harkokin Musamman, Alhaji Zaiyanu Aliero
Mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsare, Alhaji Sirajo Garba Bagudo
Mai ba da shawara kan wutar lantarki da siyasa, Alhaji Kabiru Sani (Giant)
Sakatare Dindindin, Ma’aikatar Ayyuka, Arch Saad Sakaba
- Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Alhaji Bello Yakubu (Rilisco)
Daraktan Sashen Injiniya, Ma’aikatar Ayyuka, Alhaji Sahabi Muhammad Tilli(a matsayin sakatare)
Ayyukan da aka dora wa kwamitin sun hada da: