A garin Daura, jihar Katsina, mutane bakwai ‘yan asalin garin kuma ƴan gida ɗaya s
Tuesday, 19 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

A garin Daura, jihar Katsina, mutane bakwai ‘yan asalin garin kuma ƴan gida ɗaya sun ci abinci da ake zargin yana ɗauke da guba, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum huɗu a cikin su. 
Mutanen da suka tsira sauran su uku kuma yanzu haka suna karɓar kulawa a Asibitin Koyarwa dake cikin garin Katsina.

Kawo yanzu lokacin haɗa wannan rahoton, ba bu cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru amma dai za mu kawo muku cikakken rahoto.