Ƴan bindiga sun kashe masallata 13 a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kashe mutane 13 a yayin sallar Asuba ranar Talata, a wani harin ramuwar gayya da suka kai Unguwar Mantau a karamar hukumar Malumfashi.
Kakakin ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Dr. Nasir Muazu, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina.
Ya ce, “Lamarin ya faru ne lokacin da miyagu suka kai hari domin ramuwar gayya a kan al’ummar garin. Mambobin al’umma Musulmi na cikin masallaci suna yin sallar Asuba, sai waɗannan ’yan ta’adda suka fara harbe-harbe cikin masallacin.”
Kwamishinan ya kara da cewa harin ramuwar gayya ne kan yadda al’ummar unguwar suka yi nasarar dakile su a kwana biyu da suka gabata.
A cewarsa, mutanen Unguwar Mantau sun yi wa ’yan bindigar kwanton bauna inda suka kashe da dama daga cikinsu.
Bayan wannan mummunan lamari, Muazu ya bayyana cewa jami’an tsaro sun isa yankin domin dawo da zaman lafiya.
Ya ce, “Kwamandan bangaren sojojin sama na FOB da kuma ’yan sandan Najeriya sun isa wajen domin kawar da wadannan ’yan bindiga. A lokacin damina, ’yan bindiga kan ɓuya a cikin amfanin gona domin aiwatar da munanan hari. Muna aiki tukuru domin ganin mun kamo su tare da hukunta su.”
Gwamnatin jihar ta yaba da jarumtar al’ummar Unguwar Mantau, tare da bayyana aniyar ta na ci gaba da yaki da ’yan bindiga da tabbatar da tsaro a dukkan al’ummomi.
“Hakika gwamnati na mika ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa,” in ji Muazu.