NAHCON EFCC Ta Kama Daraktocin NAHCON 2 Kan Zargin Karkatar Da Kuɗin Hajjin 2025
Wednesday, 20 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

EFCC Ta Kama Daraktocin NAHCON 2 Kan Zargin Karkatar Da Kuɗin Hajjin 2025

Hukumar EFCC ta kama daraktoci biyu na Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) bisa zargin karkatar da kuɗaɗen da aka tanadar don aikin Hajjin 2025.

Jami’an EFCC sun ce har yanzu suna tsare da su saboda sun ƙi mayar da kuɗin da aka umarce su da su dawo da su.