Gwamnatin Taraiya ta goge shafukan sada zumunta sama da miliyan 13 saboda kalaman cin zarafi
Gwamnatin ta ce ta goge shafukan ne daga kafafen sada zumunta da su ka haɗa da Facebook, Tiktok, Instagram, X da sauran su.
Daraktan sashin yaɗa labarai ma hukumar Cigaban Sadarwa da Fasahar Zamani ta ƙasa, NITDA, Hajiya Hadiza Umar, a wata sanarwar da ta fitar a yau Laraba, ta ce an goge shafuka miliyan 58,909,112 kawo yanzu.
Ta ce hakan ya biyo bayan karya dokokin sadarwa ta ƙasa.
Ta kuma yabawa Google da Tiktok bisa bin dokoki da ƙa'idojin gwamnatin Nijeriya.