Gobara a jihar kwara Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ɗan Bindiga, Abubakar Abba.
Thursday, 21 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Rahoton yace gobarar ta tashi ne sakamakon wani mutum da ke daya daga cikin shagunan katakon da abin ya faru a cikinsu ya bar wutar girki ba tare da ya kashe ta gaba daya ba, inda daga baya ta sake kunnawa har tayi sanadin tashin gobarar tare da yaduwa zuwa shagunan da ke kusa.

Kodayake ba a san adadin dukiyar da aka yi asararta nan take ba, sai dai yan kasuwar sun shiga wani hali na damuwa saboda mummunar asarar da suka yi ta miliyoyin naira.

Shugaban Sashen Yada Labarai na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Hassan Hakeem Adekunle, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ma’aikatansu sun yi nasarar shawo kan gobarar kafin ta isa wani sashe na kasuwar da ake sayar da dabbobi.