Hukumar EFCC na Neman Sirikin Atiku Ruwa a Jallo Kan Zargin Almundahana
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC na neman Abdullahi Bashir Haske ruwa a Jallo kan zargin almundahana da karkatar da wasu kuɗaɗe, lamarin da ya tashi hankalin mutane.
Hukumar ta fitar da Sanarwar neman da take masa ne a jiya Alhamis a shafinta na yanar gizo, inda dele Oyewale ya sa ma takardar hannu.
Jaridar Rariya Online ta gano Abdullahi Bashir Haske Sirikine ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar .
Hukumar ta bukaci wanda ake tuhuma yayi gaggawan bayyana kansa a Hedkwatart dake babban birnin tarayya, Abuja.