Rashin Tsaro a kasa Rashin kyawun hanyoyi ke hana sojoji yaki da ta’addanci cikin sauri -injji CDS Musa
Friday, 22 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Rashin kyawun hanyoyi ke hana sojoji yaki da ta’addanci cikin sauri -injji CDS Musa 


Babban Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce rashin hanyoyi masu kyau da barazanar bama-bamai na ƙasa (IEDs) na hana sojoji kai farmaki cikin gaggawa a wuraren hare-hare.

Ya bayyana cewa ‘yan ta’adda na samun kuɗi ta hanyar zinari da tallafin wasu mutane daga ciki da wajen ƙasa. Haka kuma, jinkirin shari’a da sakin masu laifi na rage ƙarfin sojoji.

Sai dai ya nuna nasara wajen kama manyan jagororin ƙungiyar Ansaru tare da haɗin gwiwar rundunonin tsaro, kuma ya sanar da shirin taron hafsoshin tsaron Afirka don ƙara haɗin kai da musayar bayanai.