Tinubu ya bukaci ’Yan Najeriya dake zaune a kasashen waje kada su guji kasarsu, Najeriya na farfadowa a mulkinsa.
Friday, 22 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Tinubu ya bukaci ’Yan Najeriya dake zaune a kasashen waje kada su guji kasarsu, Najeriya na farfadowa a mulkinsa. 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da kada su guji ƙasarsu, yana mai cewa Najeriya tana kan tafarkin farfaɗowa. Ya bayyana haka ne a wajen taron ’yan Najeriya a Japan, inda ya ce gwamnati ta inganta harkokin fasfo, tattalin arziki da kiwon lafiya.

Tinubu ya jaddada cewa gina ƙasa ba na gwamnati kaɗai ba ne, sai da haɗin kai na kowa. Ayau News ta ruwaito Shugaban Ƙungiyar ’Yan Najeriya a Japan, Emeka Ebogota, ya nuna goyon bayan su ga manufofin gwamnatin Tinubu.