Wani ɗalibi a Abubakar Tatari Ali Polytechnic Bauchi Ya Rasa Ransa A Hannun Ɓarayi
Friday, 22 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Wani ɗalibi a Abubakar Tatari Ali Polytechnic Bauchi Ya Rasa Ransa A Hannun Ɓarayi

Wani ɗalibi a Abubakar Tatari Ali Polytechnic (ATAP) da ke Bauchi ya rasa ransa bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidan ɗalibai da tsakar dare.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a misalin ƙarfe uku na dare, inda bata-garin suka shiga ɗakuna ɗaki-ɗaki suna kwace wa ɗalibai, kafin daga bisani su daba wa ɗalibi mai suna Samuel Mbami, ɗalibin Mass Communication a matakin ND II, wuka, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

Rahotanni daga makarantar sunyi nuni da cewa tuni an ɗauki matakan tsaro tare da haɗa kai da hukumomin tsaro domin kwantar da hankali da kuma hana ɗalibai ɗaukar doka a hannunsu.

Wannan dai ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wani hari makamancin haka a Federal Polytechnic Bauchi, duk da cewa ba a samu mutuwa ba a wancan lokacin.

-Zamani TV