’Yan Arewa a Kasuwar Alaba Rago, shahararriyar kasuwar ’yan Arewa a Jihar Legas sun roki gwamnatin jihar ta biya su diyya kan asarar da suka yi sakamakon rushe kasuwar da gwamnati nta yi.
Monday, 25 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

’Yan Arewa a Kasuwar Alaba Rago, shahararriyar kasuwar ’yan Arewa a Jihar Legas sun roki gwamnatin jihar ta biya su diyya kan asarar da suka yi sakamakon rushe kasuwar da gwamnati nta yi.

Sun bayyana cewa asarar da suka tafka ta haura Naira biliyan 20 bayan Gwamnatin Legas ta rusa masallatai sama da 40 da shaguna kimanin 3,000 a Kasuwar wadda suka kafa shekara 45 da suka gabata a jihar.—

A karo na biyu a ’yan kwanakin nan mahukunta a Jihar Legas suka rushe sassa da dama na kasuwar, wadda ta yi fice da kasuwancin kayan abinci da dabbobi da karafa da sauran kayan masarufi, wacce Hausawa suka kafa a shekarar 1979.

A cikin watan Mayun 2024, jami’an hukumar ’yan sandan jihar Legas sun mamaye kasuwar, inda suka ce an gudanar da aikin ne domin kawar da bara-gurbi a kasuwar.

Karin bayani: https://trustradio.com.ng/ha/rushe-kasuwar-alaba-rabo-yan-arewa-sun-bukaci-a-biya-su-diyya/