Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayyana shirinta na kafa rundunar yaki da ta’addanci mai dauke da sojoji 260,000 domin tunkarar barazanar tsaro da ke kara ta’azzara a yankin.
Tuesday, 26 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayyana shirinta na kafa rundunar yaki da ta’addanci mai dauke da sojoji 260,000 domin tunkarar barazanar tsaro da ke kara ta’azzara a yankin.

Shugaban ECOWAS, Omar Alieu Touray, wanda wakilinsa Abdel-Fatau Musah ya gabatar da jawabi a taron shugabannin rundunonin tsaro na Afirka da aka gudanar a Abuja, ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin dakile ayyukan ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

“Babu wani yanki a Afirka da ya tsira daga ta’addanci, rikice-rikicen cikin gida da kuma koma-baya ta fannin ci-gaba,” in ji Musah.

ECOWAS ta ce za ta bukaci dala biliyan 2.5 a kowace shekara domin tallafa wa rundunar da kayan aiki da kudaden gudanarwa. Ana sa ran Ministocin kudi da na tsaro za su gana a ranar Juma’a domin kammala tsarin yadda za a samar da kudaden.

Touray ya ce yankin Sahel ya fi kowanne yanki fama da ta’addanci, inda ya ce kashi 51 cikin 100 na mutanen da suka mutu sakamakon ta’addanci a duniya a shekarar 2024 sun fito ne daga yankin.

A yayin da ECOWAS ke ci gaba da kokarin kafa rundunar sojoji 5,000 karkashin tsarin tsaro na Afirka, ana sa ran sabuwar rundunar za ta taimaka wajen kara karfin yaki da ta’addanci.