Gwamnan Jahar kebbi Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya lashi takobin cigaba da Baiwa jami'an tsaro goyon Bayan domin shawo Kan matsalar Tsaro.
Kauran Gwandu ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro da ya gudana a dakin taro na masaukin Shugaban kasa dake babban Birnin jaha Wanda dandalin tuntuba na dattawan jaha ya shirya hadin guiwa da gwamnatin jaha