Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana damuwa kan hatsarin jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna wanda ya faru a ranar Talata da safe, inda ya haifar da damuwa ga wadanda lamarin ya faru da su.
An ruwaito cewa hatsari ya faru ne tare da matafiya jin kaɗan bayan ya bar Abuja da misalin ƙarfe 11 na safe zuwa Kaduna.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Kwamishinan yaɗa labaran jihar Malam Ahmed Maiyaki a jiya Talata a Kaduna.