Gwamna Radda na Katsina ya bayar da tallafin naira 500,000 ga duk magidancin da harin kauyen unguwar Mantau ya shafa
Wednesday, 27 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamna Radda na Katsina ya bayar da tallafin naira 500,000 ga duk magidancin da harin kauyen unguwar Mantau ya shafa yayin farmakin ‘yan bindiga kan masallata a yankin Malumfashi.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin gina wa kauyen hanya da asibiti domin taimaka wa jamaar kauyen gina sabuwar rayuwa bayan mummunan harin na yan bindiga.

Shin ya kuke ganin wannan mataki wajen tausasa zukatan mutanen da suka fusata saboda gazawar gwamnati wajen kare rayuwarsu?