Da Ɗumi-Ɗumi:
Barayin daji sun shiga ƙauyen Ɗantankari, sun buɗewa mutane wuta a wata majalissa, sun harbi mutane da dama, wanda ba a kai ga tantance adadinsu ba, a Karamar Hukumar Ɗandume ta Jihar Katsina.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa, suna roƙon jama’a da a sanya su cikin addu’a tare da neman Allah ya kawo masu ɗauki.
Allah ya kawo Mafita!!..