Gwamnatin Jihar Kebbi ta naɗa Sanusi Mika'ilu Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru
Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dr. Nasir Idris, ya amince da naɗin Alhaji Sanusi Mika'ilu Sami a matsayin sabon Mai Martaba Sarkin Zuru.
Yayin mika takardar naɗin a ranar Alhamis a garin Zuru, Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Hon. Garba Umar Dutsin-Mari, ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ga shawarar kwamitin zaɓen Sarkin Zuru.
Ya ce daga cikin 'yan takara uku da suka nemi sarautar kuma aka tantance su ta hannun kwamitin zaɓen masarautar Zuru, Alhaji Sanusi Mika'ilu Sami ne ya samu mafi yawan ƙuri’u.
Kwamishinan ya bayyana cewa an naɗa sabon Sarkin ne biyo bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Zuru, Alhaji Muhammad Sani Sami Gomo II, wanda ya rasu a ranar 16 ga watan Agusta, 2025 a asibiti da ke birnin London.
Dutsin-Mari ya gode wa Gwamnan Jihar Kebbi bisa amincewar da ya yi na naɗa sabon Sarkin, tare da kira ga sabon Basaraken da ya tabbatar da cancantar da ake masa.
Ya kuma shawarci sabon Sarkin da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya da tsoron Allah.
Sa hannu:
Ahmed Idris
Sakataren Yada Labarai na Musamman ga Gwamnan Jihar Kebbi