Ministan tsaron Nijeriya Bello Matawalle ya sake jaddada goyon bayan Nijeriya ga hadin guiwar nahiyar.
Friday, 29 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Matawalle ya sake jaddada goyon bayan Nijeriya ga hadin guiwar nahiyar

Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya Dr Bello Muhammad Matawalle, ya tabbatar da cewa kasar za ta ci gaba da mara baya ga hadin kan nahiyar Afrika a yunkurin samar da zaman lafiya da tsaro.

Da yake jawabi a Abuja, yayin bikin girmamawa da aka shirya wa mahalarta taron shugabannin hafsoshin tsaron Afrika na shekarar 2025, ministan ya ce hadin kai da kuma aiki tare sune manyan ginshikan nahiyar wajen yaki da matsalolin tsaro.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar a ranar Alhamis, Matawalle ya ce: “A daren yau ba don yaki muka taru ba, sai don murna da biki. Mun zo ne domin tunawa da irin dogon zangon da muka ci, girmama sadaukarwar da muka yi don zaman lafiya, da kuma tunasar da kanmu irin aikin da ya rage wajen gina nahiyar Afrika mai aminci.”

An gudanar da taron daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Agusta, inda ya hada shugabannin tsaro daga sassan nahiyar.Tattaunawar ta mayar da hankali kan tsaron iyakoki, yaki da ta’addanci, tsaron teku da kuma amfani da sabbin fasahohi a ayyukan soji.

Matawalle ya yaba wa hafsoshin da suka halarci taron bisa abin da ya kira jajircewarsu wajen kare mulkin kasashe da kuma tabbatar da daidaito a yankin. Ya ce zuwansu Nijeriya alama ce ta zumuncin da ke tsakanin kasashen Afrika.

Ya kara da cewa “Tare za mu iya gina Afrika inda kowane ɗan kasa zai rayu cikin tsaro da mutunci.” Ministan ya bukaci shugabannin tsaro su rungumi hadin kai tare da tsayawa kan dabi’un dimokradiyya, adalci da mutunta hakkin ɗan'adam.

Taron ya kuma tattauna hanyoyin karfafa hulda tsakanin farar hula da soji, musamman wajen sayen kayan inganta tsaro da harkar sufuri. Mahalarta taron sun jaddada muhimmancin hadin guiwar yankuna wajen tabbatar da tsaron manyan ruwan tekun Afrika.

Matawalle ya daga tare da jijjiga wani kofi a matsayin addu’ar samun nahiyar da za ta kasance cikin zaman lafiya, inda ya roki shugabannin tsaron su ci gaba da rike zumuncin da suka kulla a taron. “Allah ya sa hadin gwiwar da muka yi a nan ya samar da sakamako fiye da wannan taron,” in ji shi.