Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiyar ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya zargi gwamnoni da jawo matsaloli a Najeriya.
Farfesa Usman Yusuf ya ce gwamnoni na boye wa Shugaba Bola Tinubu gaskiya game da halin tsananin wahalar da ake ciki a Najeriya.
Farfesan ya bayyana hakane a wata hira da ta yi a wani gidan talabijin, yana mai cewa gwamnoni na karɓar kuɗaɗe masu yawa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, amma ba'a ga wani abin a-zo-a-gani da suke yi da kuɗin ba.
Ya ce sama da kashi 80 cikin 100 na matsalolin ƙasar gwamnoni ne ke jawo su, saboda sun gaza amfani da albarkatun da aka tanadar wa jama’arsu.