Wani sabon hatsarin kwale-kwale ya sake aukuwa a ƙauyen Ruggar Buda, Rafin Dartanja, ƙaramar hukumar Shagari ta Jihar Sokoto, lamarin da ake tsoron ya yi sanadiyyar mutuwar fasinjoji da dama.
Wannan mummunan lamari ya sake jefa al’umma cikin jimami, inda ya zama hatsarin ruwa na uku da ya faru a Sokoto cikin wata guda.
Mai ba wa Gwamnan Sokoto shawara kan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, Aminu Liman Bodinga, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce jami’an SEMA sun isa wajen domin gudanar da aikin ceto da kuma binciko wadanda hatsarin ya rutsa da su, tare da haɗin gwiwar hukumar NEMA da NIWA.
Rahotanni sun ce kwale-kwalen na ɗauke da fasinjoji da dama kafin ya kife, inda dukkaninsu suka fada cikin ruwa. Yanzu haka adadin waɗanda suka rasu bai kai ga tabbaci ba, sai dai majiyoyi na nuni da cewa an rasa rayuka da yawa.
Hatsarin ruwa ya zama ruwan dare a Sokoto, inda masana ke danganta lamarin da rashin kwale-kwale na zamani, raunin dokokin tsaro, da kuma rashin kayan kariya irin su life jacket.
Al’ummomin yankunan da ke dogaro da hanyoyin ruwa suna ci gaba da kira ga hukumomi da su dauki matakin gaggawa don dakile asarar rayuka.
Daga cikin matakan da ake sa ran gwamnati da hukumomin tarayya za su dauka akwai tsaurara ka’idojin tsaro, samar da kwale-kwale na zamani, da kuma wadatar da fasinjoji da kayan kare rai.