Wata kotu a kasar thailand ta tsige firaminista Paetongtarn Shinawatra da mukarraban ta ayau sakamakon rikon sakainar kashin da tayiwa iyakar dake tsakanin kasar da cambodia lamarin da acewar kotun hakan ya jefa kasar cikin rikicin siyasa.
Friday, 29 Aug 2025 00:00 am

Nagari Radio

Wata kotu a kasar thailand ta tsige firaminista Paetongtarn Shinawatra  da mukarraban ta ayau sakamakon rikon sakainar kashin da tayiwa iyakar dake tsakanin kasar da cambodia lamarin da acewar kotun hakan ya jefa kasar cikin rikicin siyasa.

fentotan wacce ta kasance ya ga tsohon firaminista Thaksin Shinawatra an dakatarda ita ne a watan da yagabata bayan zargin ta da rashin tabuka wani abin azo gani lokacin da aka bukaceta domin tattaunawa da shugaban kasar cambodia hun sen.

hukuncin da kotun mai alkalai 9  suka jagoranta ya bayyana karara irin matakin da kasar ke dauka na hukunta shugaban da bai biyar muradu da kuma dokokin kasa wanda a cewar alkalan hakan na iya jefa kasar cikin wani mummunan yanayin rikicin siyasa

a cewar wani alkali daga cikin alkalan da suka yanke wannan hukuncin wannan lamarin ya sanya rashin yarda duba da cewa an fifita son rai fiyeda bukatun kasa lamarida ya sanya akayi zarginta da hada hannu da kasar cambodia

hakama an ruwaito cewa yan majalisun jam'iyyar conservative sun zargeta da dukawa cambodia tareda rena dakarun kasa  abinda suka kira a matsayin kayarda darajar kasa.

sai dai firaministar ta musanta zarge zargen kuma yan majalsiun jam'iyyarta sun bayyana cewa tayi iya kokarinta wajen kare martabar kasa.