In Zaka yi Shirmenka Ka Daina Haɗawa da Lamarin Tsaro, Matsalar Tsaro ba Abun Siyasa Bane — Ribado ga Elrufa'i
Monday, 01 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

In Zaka yi Shirmenka Ka Daina Haɗawa da Lamarin Tsaro, Matsalar Tsaro ba Abun Siyasa Bane — Ribado ga Elrufa'i 

Gwamnatin Tinubu Ta Mayar Da Martani Kan Ikirarin El-Rufai Na Biyan ‘Yan Bindiga Kudin Fansa

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ta hannun Ofishin Mai Ba da Shawara Kan Tsaron Kasa (ONSA), ta karyata ikirarin tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya yi cewa gwamnati na biyan kudin fansa ko ba wa ‘yan bindiga wasu rangwame.

El-Rufai ya yi wannan magana ne a wata tattaunawa ta talabijin a ranar Lahadi, inda ya ce ONSA ke jagorantar irin wannan tsari.

Sai dai a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja ranar Litinin, mai dauke da sa hannun kakakin ONSA, Zakari Mijinyawa, ofishin ya bayyana ikirarin a matsayin “magana maras tushe”, yana mai jaddada cewa ba a taba yin haka a karkashin wannan gwamnati ba.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin Tinubu ta sha gargadin ‘yan Najeriya kan biyan kudin fansa, tare da bayyana cewa dakarun soji sun hallaka shahararrun shugabannin ‘yan bindiga a Kaduna, ciki har da Boderi, Baleri, Sani Yellow Janburos, Buhari da Boka.

Haka kuma, an yi nasarar cafke manyan shugabannin kungiyar Ansaru, yayin da wasu jami’an tsaro suka sadaukar da rayukansu a kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankunan Igabi, Birnin Gwari da Giwa.

ONSA ta yi kira ga ‘yan siyasa da su guji jawo cibiyoyin tsaro cikin rikicin siyasa, tana mai nanata cewa yaki da ‘yan bindiga ya kamata ya kasance na hadin gwiwa, ba wani dandali na neman yabo na siyasa ba.

Sanarwar ta ce “Ikirarin El-Rufai ba gaskiya ba ne. Ba a taba samun wani lokaci da ONSA ko kuma wani bangare na wannan gwamnati suka biya kudin fansa ko suka ba wa ‘yan ta’adda wani abin rangwame.

Akasin haka, tun farko wannan gwamnati ta dauki matakai guda biyu: farmaki na soja da kuma tattaunawa da al’umma domin magance korafe-korafe. Wannan ya kawo sauki a yankuna da suka dade suna fama da ta’addanci, musamman a Kaduna.”

Sanarwar ta kuma kara da cewa nasarorin da aka samu wajen kakkabe shugabannin ‘yan bindiga da kama shugabannin Ansaru suna da yawa, duk da cewa wasu jami’an tsaro sun rasa rayukansu.

“Don haka abin takaici ne ga tsohon gwamna irin El-Rufai ya yi watsi da wadannan sadaukarwa a kafafen watsa labarai,” in ji ONSA.

A karshe, ONSA ta bukaci a daina amfani da tsaron kasa wajen yin siyasa, tana mai jaddada cewa yaki da ‘yan bindiga aiki ne na kowa da kowa.