Kotu a Finland ta yanke wa jagoran Biafara Simon Ekpa hukuncin shekara 6 a gidan yari
Monday, 01 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Kotu a Finland ta yanke wa jagoran Biafara Simon Ekpa hukuncin shekara 6 a gidan yari 

Kotu ta Päijät-Häme da ke Finland ta yanke wa Simon Ekpa, mai rajin kafa ƙasar Biyafara, hukuncin shekara shida a gidan yari kan laifukan ta’addanci.

Kotun ta same shi da laifin tayar da zaune-tsaye da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyar ta’addanci.

A cewar jaridar YLE ta Finland, kotun ta bayyana cewa Ekpa ya yi amfani da “yawan mabiyan da yake da su a kafafen sada zumunta” wajen hura tarzoma a yankin kudu maso gabashin Najeriya tsakanin watan Agustan 2021 da Nuwamban 2024.

Kotun ta kuma gano cewa Ekpa babban jigo ne a wata ƙungiyar ‘yan a ware masu ɗaukar makami, wadda burinta shi ne raba Najeriya don kafa ƙasar Biyafara.

Haka kuma kotun ta tabbatar da cewa Ekpa ya samar wa wasu ƙungiyoyi makamai, bama-bamai da harsasai “ta hanyar  sadarwa da yake da ita a yankin”, sannan an kuma same shi da laifin ƙarfafa mabiyansa a dandalin sada zumunta na X da su aikata laifuka a Najeriya.