Gwamna Bago na Jihar Neja Ya Sauke Dukkan Kwamishinoninsa da sauran Manyan muƙamai A Jihar
Monday, 01 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamna Bago na Jihar Neja Ya Sauke Dukkan Kwamishinoninsa da sauran Manyan muƙamai A Jihar

Gwamna Umaru Mohammed Bago na jihar Neja ya amince da rusa dukkan kwamishinoni da sauran manyan mukamai na siyasa a jihar.

A cewar sanarwar, Shugaban ma’aikata, mataimakin shugaban ma’aikata, sakataren gwamnatin jiha da kuma manyan jami’an ofishin gidan gwamnati ne kadai aka cire su kuma za su ci gaba da rike mukamansu.