Maudu’i Korafi Kan Matsalar Tsaro a Karamar Hukumar Augiu
Mai Girma Gwamna,
Ina rubuto wannan takarda ne don nuna matukar damuwa da bakin ciki game da halin rashin tsaro da ake fuskanta a Karamar Hukumar Augie. Lamarin ya kai wani mataki mai tayar da hankali, musamman da yawaitar hare-haren 'yan bindiga da sace-sacen mutane.
Wani Al’amari na Musamman:
A ranar 30 ga Agusta, 2025, a kauyen Dudaye, mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga.
Tasirin Lamarin
Mutane da dama sun bar gidajensu
Harkokin kasuwanci sun tsaya cik
Tsoro da firgici sun mamaye zukatan jama'a