Kungiyar Likitocin Masu Ƙwarewa a Najeriya (NARD) ta bai wa gwamnatin tarayya wa adin kwanaki goma don ta cika bukatun da likitocin suka dade suna nema, in ba haka ba za su tsunduma yajin aiki a duk faɗin ƙasar nan.
Monday, 01 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Kungiyar Likitocin Masu Ƙwarewa a Najeriya (NARD) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki goma don ta cika bukatun da likitocin suka dade suna nema, in ba haka ba za su tsunduma yajin aiki a duk faɗin ƙasar nan.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugabancin ƙungiyar ya fitar bayan taron gaggawa na majalisar zartarwa ta ƙasa da suka gudanar ta hanyar taron bidiyo a ranar Lahadi