Gwamnatin Soji Ta Burkina Faso Ta Hárámta Lúwáɗí A Ƙasar
Gwamnatin sojoji a Burkina Faso ta amince da wata sabuwar doka da ta haramta áurán jínsí tare da sanya hukuncin da zai kai shekaru biyar a gidan yari.
Tun kafin juyin mulkin da sojoji suka yi shekaru uku da suka wuce, áurén jínsí bai kasance wani abu da doka ta hana shi ba a ƙasar, sai dai yanzu Burkina Faso ta shiga jerin ƙasashen Afirka sama da 30 da suka haramta áurén jínsí a hukumance.